Matsalar rashin inganci layukan sadarwa a Birtaniya

Wani rahoto da aka fitar akan samun layukan sadarwa masu inganci a filin jiragen kasa na Birtaniya ya nuna cewa akasin haka ake samu.

Binciken da wata kungiya da ake kira Global Wireless Solutions ta yi ya gano cewa ba 'a samun layin sadarwa me inganci a waya daya daga cikin wayoyin uku, haka a cikin kira bakwai , daya daga ciki ba shi da inganci.

Kungiyar ta ce injiniyoyinta sun gudanar da bincike kan layukan dogo goma da jama'a suka fi amfani da su a wajen garin Landan da kuma cikin birnin.

Sun kuma yi amfani da wayoyin Samsung GalaxyS4s wajen tattara bayanai ta hanyar amfani da kartin manyan kamfonin wayoyin salula hudu dake Birtaniya.

Sai dai binciken ya gano cewa kamfanonin EE da 02 da Vodafone sun matukar dogara ne akan naurar 2G domin hada mutane su yi magana da juna.

Hakkin mallakar hoto EPA

Haka kuma mutane da ke amfani da irin wannan naura ta 2G zasu rika samun layin sadarwa mara inganci ba.

Wani mai sharhi kan sadarwa ya ce abu ne mai wuya naurar 2G ta isar da kira ko sako cikin sauri kamar sauran takwarorinta na zamani.

Sai dai kamfanin EE ya ce yana alfahiri da naurar 4G da yake amfani da ita kuma yana kokarin ganin cewa ya inganta ayuikansa a hanyoyi da kuma layukan dogo dake fama da rububin jama'a.