Boko Haram: Amurka ta nuna shaku kan tsaigata wuta

Hakkin mallakar hoto AP

Amurka ta ce bata da tabbacin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka bada sanarwar cewa an kulla tsakanin sojojin Nigeria da kuma mayakan kungiyar nan ta Boko Haram a Nigeriar.

Gwamnatin Nigeria tace yarjejeniyar ta hada- da sakin 'yan matan sakandaren nan fiye da 200 da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace watanni shida da suka gabata.

Amma sai dai kungiyar ta Boko Haram bata ce komai ba ya zuwa yanzu

An dai ce an cimma yarjejeniyar ne bayan makonnin da aka shafe ana tattaunawa a kasar Chadi

Haka kuma ana bukatar karin wata ganawar a nan gaba, domin tsara yadda za'a sako 'yan matan na Chibok.