BBC za ta wallafa wasu bayanai da Google ya cire

BBC ta ce za ta cigaba da wallafa wasu bayanai da kamfanin Google ya cire daga shafinsa karkashin sabuwar dokar nan ta yancin cire bayanai.

Dokar ta ba mutane damar neman Google ya cire wasu bayanai game da su .

Shugaban sashin kaidojin aikin jarida na BBC, David Jordana ya fadawa wani taron jin bahasin jama'a da Google ya shirya cewa BBC na ganin an yi kuskure akan yadda aka boye wasu bayanansa.

A cewarsa ya kamata a kara baiwa yancin da mutane da suke da shi na sanin abin da ya faru a baya fifiko.

Sai dai tun bayan hukuncin da wata kotu a Turai ta yanke Google ya bude wani shafi da ya ba mutane damar magana akan bayanin da suke son a cire masu.

Kotun ta ce shafuka masu alaka da juna mara muhimanci da kuma ba su da tushe be kamata sunan mutane ya rika fitowa a ciki ba.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kamfanin Google ya sanar da shafukan da lamarin ya shafa da kuma duk lokacin da ya cire wani bayani daya shafesu.

Sai dai BBC ta ce a makonin kalilan masu zuwa ne za ta soma wallafa wasu bayanai da Google ya cire.

Mr Jordan ya ce tuni Google ya sanar da su cewa ya cire bayanai 46 , ciki har da shafin Robert Peston da ke sharhi kan tattalin arziki.

Ana ganin wani da ya taba sharhi a cikin shafin Robert Peston ne ya shigar da wannan bukata.