Masu barazana a Internet na fuskantar dauri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu barazana a internet na fuskantar daurin shekaru biyu

Barazana a internet ka iya fuskantar daurin shekaru biyu a gidan yari karkashin sabbin dokoki a cewar sakataren shari'ah Chris Grayling.

Ya fadawa jaridar Mail a ranar Lahadi cewa nunnunka hukuncin daurin watanni shidan da ake amfani da shi yanzu ya nuna cewa da gaske yake wajen daukar mataki akan masu wannan halayya.

An sanar da shirin ne kwanaki bayan da aka ci zarafin wata mai gabatar da labaran gidan Talabijin Chloe Madeley a internet, wanda Mr Grayling ya nuna cewa ba daidai bane.

Kotun majistire ka iya mika irin wadannan shari'oi zuwa kotunan da ke yin shari'a akansu karkashin sabbin dokokin.

Mr Grayling ya fadawa jaridar cewa 'wadannan masu barazana a Internet din matsorata ne wadanda suke gurbata rayuwar 'yan kasa da guba'.

Ya ce ba za a yarda da wannan a shafukan sada zumunta ba.

An yiwa Miss Madeley barazana ne bayan data kare kalaman mahaifiyarta Judy Finnigan akan fyaden da wani dan wasan kwallon kafa Ched Evans ya aikata, wanda tace kalamai ne da basu cutar da kowa ba.

Babban jami'in ma'aikatar shari'ar ya kara da cewa 'dole ne mu isar da wannan sakon, na cewa idan ka yi barazana, akwai yiwuwar ka shafe shekaru biyu a gidan yari'.

Za a canja dokar ne a matsayin gyara ga kudurin kotunan masu aikata laifi ta hanyar 'yan majalisar dokoki.

Sabbin matakan za su baiwa 'yan sanda damar karin lokaci na tattara hujjoji domin gabatar da kara a gaban kotu.