'Yan Boko Haram sun mamaye garin Abadam

Yawancin mazauna garin Abadam din sun tsere zuwa Jamhuriyar Nijer, wasu kuma sun bazu zuwa sassa dabam dabam na Najeriya.

Wani wanda ya tsira daga harin ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa 'yan Boko Haram sun shiga garin ne cikin daren Alhamis a ciki motocinsu dauke da bindigogi.

Yace suna shiga garin, sai suka fara harbe mutane, suna fasa shagunansu, suna kwasar kayayyaki.

Ya kuma ce a ranar Asabar 'yan Boko Haram din sun kwace garin baki dayansa, sun kafa totucinsu ko'ina.

Ga cewarsa, akasarin mutanen garin sun ketare kogi sun tsere zuwa Jamhuriyar Nijer.

Wasu kuma sun gudu zuwa sassa dabam dabam na Najeriya yayin da wasu suka shiga daji, har yanzu ba a san inda suke ba, inji shi.

Ya ce iyayensa da wasu 'yan uwansa duk sun shiga daji, ba san yadda za a gano su ba.