Ebola: Ma'aikaciyar jinyar Spain ta ci gwajin farko

Ebola Hakkin mallakar hoto AP
Image caption kwararru sun ce sai an gudanar da gwaji a karo na biyu za a tantance ko ta rabu da cutar

Gwajin farko da aka gudanar akan ma'aikaciyar jinyar nan 'yar kasar Spain da ta kamu da cutar Ebola ya nuna ba ta dauke da kwayar cutar.

Amma bayanai na nuna cewa har sai an gudanar da gwaji a karo na biyu kamin a tabbatar da cewa Teresa Romero ta warke daga cutar.

Gwamnatin kasar ta Spain ta ce an yi amfani ne da wani ruwan jikin wadanda suka warke daga cutar da kuma wani magani da ba ta bayyana sunansa ba wajen warkar da matar.

Romero ta kamu da cutar ne a wani asibiti dake Madrid bayan da ta kula da wasu limaman coci su biyu da suma suka kamu da Ebolan.

Ita ce kuma mutum ta farko da ta kamu da cutar daga wajen Afrika a wannan annobar da ta barke.