Boko Haram: An sace dabbobi a Gwoza

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin Boko Haram da sace shanu 1,300 a Ngala

Rahotanni daga kauyen Gava a Jamhuriyar Kamaru na nuna cewar 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun sace dabbobi da dama.

Lamarin ya auku ne a daren ranar Litinin inda 'yan Boko Haram din suka shiga garin da babura suka yi awon gaba da shanu masu tarin yawa da kuma awaki fiye da 1,000.

Wani makiyayi ya shaidawa BBC cewar a tsawon lokacin da 'yan Boko Haram suka shiga kauyen basu samu dauki daga jami'an tsaro ba.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da 'yan Boko Haram suka sace shanu fiye da 1,300 a garin Ngala da ke kan iyaka da Jamhuriyar Kamaru.

'Yan Boko Haram sun yi garkuwa da daruruwan mutane abinda ya sa wasu ke ganin cewar suna bukatar dabbobi da dama domin ciyar da mutanen da suke tsare da su.

A garin na Gwoza ne dai kungiyar Boko Haram din ta yi shelar kafa daular musulunci, a watannin baya, bayan da ta kame garin, ta kuma nada sabon sarki.