Amurka ta yi na'am kan sulhu da Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gwamnati na shan matsin lamba domin ta ceto 'yan matan Chibok

Amurka ta ce bisa dukkan alamu an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Nigeria da mayakan Boko Haram.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Marie Harf ta ce a yanzu haka ana ci gaba da tattaunawa domin sako 'yan mata dalibai fiye da 200 da 'yan Boko Haram suka sace.

An soma nuna shakku game da yarjejeniyar tsagaita wuta da dakarun Nigeria suka sanar a ranar Juma'a saboda hare-haren da 'yan Boko Haram suka kai a karshen mako.

Gwamnatin Amurka ta aike da kwararrun jami'an leken asiri da jirage marasa matuka domin taimakawa jami'an tsaron Nigeria.

Fiye da watanni shida kenan da 'yan Boko Haram suka sace dalibai 'yan mata a Chibok su fiye da 200.