Ebola: Burtaniya ta tura likitoci 100 zuwa Saliyo

Britain Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Likitocin za su horas da dubban ma'aikatan lafiyar kasar ta Saliyo ne

Masana kiwon lafiya kimanin 100 daga rundunar sojin Burtaniya sun tashi zuwa kasar Saliyo a yammacin Africa domin taimakawa wajen yaki da cutar Ebola.

Ana sa ran likitocin za su horas da dubban ma'aikatan kiwon lafiya na kasar ta Saliyo inda cutar ta yi kamari, bayan da cutar ta kashe mutane sama da 4000 a kasar ta Saliyo da Guinea da kuma Liberiya.

Ya zuwa yanzu dai shugaban Ghana, John Dramani Mahama, wanda shi ne ke jagorantar kungiyar ECOWAS ko kuma CEDEAO ta yankin, ya ce an fara samun isar kayayyakin agaji zuwa kasashen da cutar ta addaba.

Tuni dai masana a fannin tattalin arziki suka fara hasashen cewa annobar cutar ta Ebola za ta iya yin tasiri a kan ci gaban tattalin arzikin kasashen da ma yankin na yammacin Africa muddin ba tashi haikan ba.