Burtaniya: Samo wutar lantarki daga Tunisia

Burtaniya Hakkin mallakar hoto
Image caption shigo da wutar lantarki mai hasken rana daga kasashen Afrika ba sabon abu bane

'Yan kasuwa a Burtaniya na neman tallafi daga gwamnatin kasar domin shigo da wutar lantarkin da ake samu ta hanyar hasken rana daga Tunisia.

Wannan shiri a cewar rahotanni, zai iya samawa 'yan Burtaniya miliyan 2.5 hasken wutar lantarki nan da shekara 2018.

Kamfanin da yake aikin samar da wutar ya ce yanzu haka ya kashe euro miliyan 10 wajen bunkasa shirin na samar da wutar ta lantarki ta hanyar hasken rana.

Yanzu haka 'yan kasuwa masu samar da wutar lantarki, na kokari su shigar da kayayyakinsu zuwa kasar ta Burtaniya daga shekarar 2017.

Wani kamfani da ake kira TuNur dake da hadin guiwa da wani kamafin Burtaniya ne yake kokarin samar da wannan shiri, inda ya ce tuni ya kashe euro miliyan 10.

A cewar kamfanin, ya kwashe shekaru uku yana tattara bayanai domin cimma wannan buri.

Rahotanni sun ce tuni majalisar dokokin kasar Tunisia ta amince da fitar ayyukan samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da hasken rana zuwa nahiyar turai dama wasu kasashe.

"Wannan shiri ne mai muhimmanci, ba sabon abu bane a kai wutar lantarki daga Afrika zuwa nahiyar turai." In ji Kevin Sara, shugaban kamfanin TuNur.