Kayan aiki da jinyar ebola sun samu

Masu fama da cutar Ebola
Image caption Masu fama da cutar Ebola

Shugaban kasar Ghana John Mahama ya ce a yanzu kayayyakin aiki da kuma na jinya sun fara isa kasashen da cutar Ebola tafi kamari a yankin yammacin Afrika.

Shugaban kasar ta Ghana wanda kuma shine shugaban kungiyar Kasuwancin Yammacin Afrika wato ECOWAS ko kuma CEDEAO, ya ce abinda ya rage a yanzu shine yadda kungiyoyi da kasashen da ke tura kayayyakin za su hada kai don ganin abubuwan da suke aikawa ba su kasance iri daya ba.

A daidai lokacinda kuma Shugaban Kungiyar ta ECOWAS ke wannan sheila, Kwararru masana kiwon lafiya kimanin dari daya daga rundunar sojan Brittaniya na kan hanyar su ta zuwa kasar Saliyo a yammacin Afrika don taimakawa wajen yaki da annobar cutar Ebola.

Adadin mutane dubu da dari biyar ne aka bayar da rahoton sun mutu sakamakon cutar ta Ebola a kasashen na Saliyo da makwabciyar ta Guninea da Liberia.

Ma'aikatan agaji sun ce, a halin da ake ciki yanzu haka an gaza ciwo kan annobar.

Karin bayani