Google zai yaki satar fasaha ta Internet

Kamfanin Google Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kamfanin Google

Kamfanin Google ya yi sauye-sauye don yaki da satar fasahar wasu.

Kamfanin Google ya sanar da wasu sauye-sauye a na'urar bincikensa a wani yunkuri na kare satar fasahar wasu ta hanyar internet.

An dade ana sukar lamirin kamfanin saboda bayar da dama da ya yi ga wasu mutane dake shiga wasu shafuka suna nadar wakoki ko fina-finai sabanin doka.

Masana'antar ta nishadantarwa ta yi tankiyar cewar kamata ya yi a kare shafukkan da suka saba ma doka a ciri wani abu a na'urar binciken ta kamfanin google.

Sabbin matakan wadanda yawancin kamfanonin tallar wakoki watau BPI suka amince da su, a maimakon haka za su rinka nuna wa masu neman wakokin da za su nada ta Internet hanyar da za su bi ta kaiwa ga wakokin da doka ta amince su nada, wadannan kuwa sun hada da bin tsari na Spotify da Google Play.

A yanzu kamfanin na Google zai rinka tsara irin wadannan wakoki a wani akwati da zai rinka fitowa a saman shafin na'urar binciken ta Google da kuma cikin wani akwati da zai rinka bulla a sashen hannun dama na shafin.

Sai dai kuma, sanya wadannan wakoki da doka ta amince wani ya nada a shafin na Google zai zamo tallar wakokin. Don haka idan masu irin wadannan wakokin suna so a sanya wakokin na su, to lallai ne su biya kamfanin na Google.

Kamfanonin tallar wakokin sun ce kodayake sun yi marhabin da wadannan sauye-sauye na kamfanin na Google, suna ganin bai dace ba a sanya masu irin wadannan wakoki su biya wasu kudade.

Wani mai magana da yawun kamfaninin tallar wakokin ya gaya ma BBC cewar, bai kamata ace, za a caji wasu kudade ba, idan dai har za a baiwa jama'a damar nadar irin wadannan wakoki.

Kamfanin na Google kuma har ila yau ya kara wasu matakan na sa ido kan na'urar bincikensa, ta yadda za su rinka boye wakokin da ba a yadda a nada ba, yayinda na'urar za ta rinka nuno wakokin da doka ta amince a nada a duk lokacin da mai neman shafin ke lalube.

Kamfanin na Google dai ya shafe shekaru da dama yana bayar da wannan kariyar, to amma a yanzu, ya sake fasalin tsarin bayar da wannan kariyar ne da nufin yaki da satar fasahar wasu.

Karin bayani