Tambuwal ya halarci taron APC a Sokoto

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tambuwal tare da Gwamna Rabiu Kwankwaso

Shugaban Majalisar Wakilan Nigeria, Aminu Waziri Tambuwal ya halarci taron masu ruwa da tsaki na 'yan jam'iyyar adawa ta APC a jihar Sokoto.

Amma dai kakakinsa, Imam Imam ya ce shugaban majalisar yananan daram a jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, kuma ya halarci taron APC ne saboda goron gayyatar da Gwamnan Sokoto, Aliyu Wamakko ya aika masa.

An dade ana alakanta Tambuwal da jam'iyyar APC amma har yanzu bai fito fili ya bayyana cewar ya fice daga jam'iyyar PDP mai mulkin kasar ba.

Sanarwar da kakakin ya fitar, ta ce har yanzu Shugaban Majalisar na tuntunbar wadanda suka dace game da makomar siyasarsa.

Masu sharhi na ganin cewar, Mr Tambuwal na bukatar komawa jam'iyyar APC a jihar Sokoto idan yanason cimma burinsa na siyasa a shekara ta 2015.