Audi mai sarrafa kan ta, ta cinye tsere

Motar kamfanin Audi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Motar kamfanin Audi

Kamfanin kera motoci na Audi na kasar Jamus ya ce motar sa samfurin RS7 ta cinye tseren da aka yi na kilomita 240 cikin sa'a guda a wurin teren motoci na Hockenheim dake kudancin Frankfurt.

Motar ta shanye sha-tale-talen tseren motocin ne cikin mintoci biyu da wasu dakikoki.

Tseren motocin an shirya shi ne don nuna kokarin da kamfanin ya yi na kawo gwajin tuki na motocin masu sarrafa kan su da kan su a kan hanyoyi. To, sai dai kuma wani kwararre ya yi kashedin cewa akwai matsaloli da dama dake bukatar nazari.

Kamfanin Motar Audi wani reshe na kamfanin Volkswagen ya kuma sanya wanu mutum ya zauna a matsayin direban motar don yin gwaji. Ya dauki tsawon karin dakikoki biyar wajen zagayen filin tseren motocin.

Daya daga cikin masu bincike na kamfanin kera motocin ya bayyana cewa ya yi imanin nan gaba mutane za su yi amfani da wannan sabuwar fasahar da aka kirkiro.

Dr Horst Glaser yace, "tuki da ba ya tattare da hadari zai zamo wani mafarki. To amma a kalla muna iya rage yawan hadurran da ake samu nan gaba,"

Gwajin tukin, ya kawar da yanayi kamar alal misali na shiga cikin cincirindon motoci. A duk lokacinda wani abu ya dauki hankalin direba, motar za ta iya sarrafa kan ta.

"bugu da kari, direban yana da lokacinda zai huta. Wannan yana nufin, hankalina yana tare da shi a duk lokacinda aka bukaci hakan."

Motar samfurin RS7 tana amfani da abubuwa kamar su kemara da na'urar bincike, da taswirar bayanai na wurare, da radion oba oba, da na'urar da za ta rinka yi ma jagora, da kuma bayanai dake kunshe cikin na'ura mai kwakwalwa wadda aka harhada cikin akwatin baya na motar.

Wannan gwaji da aka yi, ya nuna kololuwar da aka ki ta bincike bayan binciken da kamfanin ya gudanar a Amurka da Turai cikin shekaru goma sha-biyar da suka gabata.

Karin bayani