Mun aurar da 'yan matan Chibok - Shekau

Wasu daga cikin 'yan matan makarantar Chibok da aka sace Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu daga cikin 'yan matan makarantar Chibok da aka sace.

Kungiyar Boko Haram ta karyata cewa ta cimma sulhu da gwamnatin Nigeria.

A wani faifan bidiyo da shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya fitar, wanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya samu, shugaban kungiyar ya ce 'yan matan nan na Makarantar Chibok da kungiyar ta yi awon gaba da su, sun Musulunta, kuma tuni aka aurar da su.

Sanarwar ta Shekau dai ta saba da ikirarin da gwamnatin Nigeria ta yi na cewa ta cimma sulhu da 'yan Boko Haram kuma tana shirin karbo 'yan matan Chibok daga hannun Boko Haram.

Shugaban na Boko Haram Abubakar Shekau ya kuma ce kungiyar sa ce ke rike da wani dan kasar Jamus da aka sace a cikin watan Yulin da ya gabata a garin Gombi na jihar Adamawa.

Wannan faifan bidiyon na zuwa ne bayan da sojojin Nigeria suka bayar da sanarwar cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da 'yan kungiyar a ranar 17 ga watan Oktoba domin kawo karshen hare-haren Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto afp

Wani babban jami'i a fadar gwamnatin Nigeriar ya kuma ce yarjejeniyar da aka cimma ta kunshi sakin 'yan matan na Chibok wadanda sace su ya ja hankalin kasashen duniya da dama.

Wani wanda yake ikirarin yana magana da yawun kungiyar Boko Haram, Danladi Ahmadu ya bayyana wa wasu kafofin yada labarai cewa tabbas gwamnatin Nigeriar na kan tattaunawa da 'ya'yan kungiyar.

Sai dai Abubakar Shekau a cikin sabon bidiyon ya ce ba sa tattaunawa da kowa.

Shugaban na Boko Haram ya kuma bayyana cewa bai san wani da ake kira Danladi ba

Abubakar Shekau Ya bayyana cewa: 'Ba mu yi sulhu da kowa ba, ba mu yi sulhu da Chadi ba, ba mu yi sulhu da Kamaru ba, ba mu yi sulhu da Nigeria ba, karya ne, ba za mu yi ba.'

Ba a dai san lokaci da kuma a ina ne aka nadi wannan sabon bidiyon ba.

Abubakar Shekau ya kuma kara da cewa babu maganar duk wata tattaunawa a nan gaba.

A baya dai gwamnatin Nigeria ta sha cewa ta kashe Abubakar Shekau, batun da shekau ya musanta.

Karin bayani