Boko Haram: 'Yan gudun hijira sun koka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mata da kananan yara na cikin mawuyacin hali

'Yan gudun hijirar da suka tserewa rikicin Boko Haram a Nigeria na ci gaba da kokawa game da kuncin rayuwar da su ke fuskanta a wuraren da suka koma.

Dubban 'yan gudun hijirar da suka tsallaka zuwa Jamhuriyar Kamaru sun bayyana cewar suna cikin mawuyacin hali sakamakon rashin samun isashen tallafi daga gwamnatin Nigeria.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar a garin Fotokol na Kamaru sun ce mata da dama sun haihu a sansanonin 'yan gudun hijira cikin yanayi mara tsafta.

A cewarsu, mutane na ta mutuwa sakamakon yunwa da cututtuka a sansanoni daban daban na al'ummar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.

A yanzu haka akwai 'yan gudun hijira fiye da 43,000 da suka shiga cikin Kamaru saboda hare-haren 'yan Boko Haram.