Karuwar jirage marasa matuka a Burtaniya

Drones Hakkin mallakar hoto INFOTRON
Image caption Masu aikata ayyukan ta'addanci za su iya amfani da shi wajen kai hare hare

Karuwar da ake samu ta yin amfani da jirage marasa matuka a Burtaniya na barazana ga tsaron kasar da kuma sirrin jama'a, wani rahoto ya ce.

Hukumar tsare -tsare ta jami'ar Birmingham wacce ta fitar da rahoton, ta ce akwai yuwuwar kungiyoyin 'yan ta'adda su yi amfani da fasahar wajen kai hare hare.

Sai dai duk da haka, rahoton bai kore dumbin amfanin da jiragen marasa matuka za su kawo ga ci gaban tattalin arzikin da fannin tsaron kasar ba.

Amma rahoton ya ce akwai bukatar a dauki matakan kare sararin samaniya da kuma sirrin 'yan kasar.

"Akwai barazana kwarai tattare da yadda mutane suke yawan amfani da jirage marasa matuka." In ji Sir David Omand, wani tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar Burtaniya.

Ya kuma kara da cewa "ko dai a yi amfani da su wajen aikata manyan laifuka ko kuma na ayyukan ta'addanci."

Har ila yau rahoton ya ce abi mafi sauki ne ayi amfani da jiragen wajen kai hare hare a kasuwanni ko kuma filayen wasanni.

Sai dai duk wadannan kalubale, jirage marasa matuka, sukan taimaka wajen gano masu sace - sace ko 'yan fashi ko kuma masu farautar namun dajin da aka haramta farautarsu.

Baya ga haka, masu sana'ar daukan hotuna za su iya amfani da jiragen wajen samun hotunan fitattun mutane ba tare da sun wahala ba.