An yi artabu da dan bindiga a Canada

Harbe harbe a  Canada Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Harbe harbe a Canada

An gudanar wani gagarumin aikin tsaro a Ottawa, babban birnin kasar Canada, bayan da aka yi hari a wurare uku, ciki har da majalisar dokoki.

Wani dan bindiga ya yi harbi ya kashe wani soja da ke gadi a wani wurin tunawa da yake-yake, kafin daga baya 'yan sanda su fafare shi zuwa ginin majalisar dokoki da ke kusa, wadda a halin yanzu aka hana mutane zirga-zirga a wurin.

Majalisar ministocin Canadar tana zama ne a cikin ginin, a lokacin da suka ji karar harbe-harbe.

Daga bisani an harbe dan bindigar har lahira.Pirayim Ministan Canada, Steven Harper, yayi tir da harin da ya kira abin kyama.