'Filin jirgin saman Jigawa ba shi da amfani'

Hakkin mallakar hoto google
Image caption 'Yan hamayyar sun ce mazauna jihar na fama da rashin ilimi da lafiya

'Yan hamayya a jihar Jigawa da ke Nigeria sun ce filin jirgin saman da shugaba Goodluck Jonathan ya bude a jihar ranar Talata ba shi da amfani.

'Yan hamayyar sun kara da cewa mazauna jihar na fama da matsalolin rashin wutar lantarki da rashin ilimi da kiwon lafiya, don haka a cewarsu, wadannan matsaloli suka kamata a bai wa muhimmanci ba filin jiragen sama ba.

Wani babban dan jam'iyyar adawa ta APC a jihar, Faruka Adamu Aliyu ya shaida wa BBC cewa idan ban da shugaba Goodluck Jonathan da ya sauka a filin, gwman jihar Sule Lamido ne kawai ke amfani da shi.

Sai dai jam'iayyar PDP da ke mulkin jihar ta ce bude filin jiragen saman zai bunaksa tattalin arziki da ci gaban jihar.

Karin bayani