NASA ta kaddamad da laburare na amo

Kumbon Amurka Hakkin mallakar hoto SPACEX
Image caption Kumbon Amurka

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA ta kaddamad da laburare na amo ko saututtuka da muryoyi kyauta ga masu bukata.

Dan yanki na amo da sauti da muryoyi 60 da hukumar ta NASA ta fitar a yanzu sun hada da muryoyin 'yan sama jannati da na kumbon da aka tura sararin samaniya.

An fitar da muryoyi na tarihi na tafiye-tafiyen da 'yan sama jannati suka yi don bincike a sararin samaniyar wadanda aka ajiye a laburare na sautin da mutane za su iya saurara su kuma nada kyauta.

An sanya na'uoi 60 a asusun ajiyar saututtuka na hukumar saboda mutane, to amma babu wani wanda ya saurara da ya bar wani sharhi a game da su.

Irin mu'ammala da tuntubar juna da 'yan sama jannatin suka rinka yi kamar lokacinda "Houston ya rinka cewa, muna fuskantar matsala" da kuma "Mikin ya sauka" duk za a iya sauraren su, akwai kuma irin motsin da kumbon ke yi misali a kan Wata da karar buraguzai da za a iya saurara.

A sararin samaniyar kan ta, sauti ba ya zuwa ko'ina saboda babu iska a can.

Hukumar binciken sararin samaniyar tace, "za ka iya jin karar saukar Kumbo a duk lokacinda aka bugo maka waya, idan har ka nade shi a matsayin amon wayar ka ta salula."

Ko kuma za ka ji kalamai na tarihi na Houston, lokacinda yake cewa "muna da matsala, a duk lokacinda ka yi wani kuskure a Komputar ka."

Wannan laburare na sauti da maganganun 'yan sama jannati, kusan irin laburare ne na hotuna na 'yan sama jannatin da ziyarar binciken da suka kai sararin samaniya, wanda shi ma za a iya samun sa kyauta ga kowa.

Hukumar binciken sararin samaniyar ta NASA ta kaddamar da asusun na ta a lokaci daya da kamfanin sada zumunta ta internet watau twitter ya baiwa masu amfani da shafin damar amfani da sauti wajen hudda da abokansu.

Karin bayani