'Yan jarida za su yaki Hamada a Nijer

Hamadar Sahara a Nijer Hakkin mallakar hoto Almoustapha Alhacen
Image caption Hamadar Sahara a Nijer

A Jamhuriyar Nijar, yau aka shiga rana ta biyu na wani taron kara wa juna sani na kwanaki uku da hukumar kare muhalli ta shirya ga 'yan jaridu da wakilan kungiyoyin farar hula.

Taron zai yi musu bayani ne a kan irin illolin da al'amarin kwararowar hamada da sauyin yanayi ke yi ga rayuwar jama'a, ta yadda za su iya bada ta su gudummuwa wajen fadakar da jama'a.

Wata kididdiga ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi nunin cewa kimanin mutane miliyan biyu ne a duniya, zaizayar kasa da kwararar hamada ke yin illa ga rayuwar su ta yau da kullum.

Yankin Sahel yana cikin yankunan da a kowacce shekara ake fuskantar karancin abinci sakamakon illolin na sauyin yanayi, da kwararar hamada.

Karin bayani