An binne mutanen da suka mutu a Azare

Harin Bam a tashar Mota a Azare Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harin Bam a tashar Mota a Azare

A Nigeria, an yi jana'izar mutanen da suka mutu sanadiyar harin bam din da aka kai a wata tashar mota a garin Azare da ke kimanin kilomita 200 a arewa da birnin Bauchi.

Mutanen da suka shaida lamarin sun gaya wa BBC cewa mutane kusan 15 suka mutu baya ga dimbin mutanen da aka jikkata a harin da aka kai da misalin karfe goma na daren Laraba.

Rundunar 'yan sandan jihar ta shaida wa BBC cewa mutane biyar ne suka mutu.

Ma'aikatan agaji da jama'ar gari sun kwashe wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibiti.

Tashar motar ba ta da nisa daga babban ofishin 'yan sanda na yankin.

Kawo yanzu dai ba a tantance ba ko harin kunar-bakin-wake ne ko kuma dasa bam din aka yi a bakin tashar motar, wadda ita ce tashar mota mafi girma a garin na Azare.

Karin bayani