Garan bawul a majalisar ministocin Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Jonathan ya ce ministocin za su rike mukaman har sai an nada sabobi

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya gudanar da garan bawul a majalisar zartarwar kasar sakamakon murabus din ministoci bakwai suka yi.

Shugaba Jonathan, ya umurci karamin minista a ma'aikatar harkokin wajen kasar, Dr. Nurudeen Mohammed ya lura da ma'aikatar watsa labarai.

Haka kuma karamar minista a ma'aikatar harkokin waje, Farfesa Viola Onwuliru ta koma ma'aikatar ilimi a matsayin karamar minista.

Shi kuma ministan ayyuka na musamman, Tanimu Turaki shi ne zai dunga sa'ido a kan ma'aikatar kwadago.

Ministocin tsaro da na cinikayya da kuma na harkokin Niger Delta su ne za su rike ayyukan kananan ministocinsu da suka bar aiki.

Karin bayani