Karancin Ilimi na yin tarnaki ga sahihin zabe

Zabe a Nijeriya Hakkin mallakar hoto b
Image caption Zabe a Nijeriya

A Nigeria, masana sun bayyana cewa karancin ilimi game da harkokin zabe na cikin abubuwan da ke tarnaki ga yunkurin gudanar da sahihin zaben.

A cewarsu, ilmantar da al'umma tun daga shekarun yarinta shi ne mataki mai matukar muhimmanci na wayar da kan masu kada kuri'a.

Dokta John Akpoere, jagora a wata cibiya mai zaman kanta da ke kula da ilimin yara da bunkasa matasa a Nigeria, na cikin masanan da ke da irin wannan ra'ayi.

Ya ce duk da yake ana wayar da kan jama'a game da zaben matakin ilimantar da su ko kusa bai kai matakin da ya kamata a ce ya kai ba.

Karin bayani