An jefe wani matashi a Somalia

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A watan jiya ma Al-Shabaab ta yanke wa wata mace hukunci jefewa bayan an same da da laifin zina

Kungiyar al-Shabab da ke Somalia ta jefe wani matashi bayan ta same shi da laifin yi wa wata yarinya fyade.

An jefe matashin dan shekara 18 ne ranar Talata a yankin Lower Shabelle da ke kudancin kasar.

Alkalin da ya yanke hukuncin ya ce matashin ya yi wa yarinyar fyade ne bayan da ya yi mata barazanar kisa da bindiga.

A watan jiya ma, kungiyar ta Al-Shabab ta jefe wata mata bayan ta same ta da laifin yin zina a garin Barawe.

Karin bayani