Boko Haram sun sace mata da dama a Adamawa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Har yanzu ba a san adadin matan da Boko Haram suka sace ba

Rahotanni daga jihar Adamawa da ke arewacin Nigeria na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun sace mata da dama a wasu kauyuka da ke kusa da Michika.

Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa an sace matan ne kwanaki kadan da suka gabata amma sai yanzu labarin ke fitowa.

Sun kara da cewa 'yan kungiyar sun kai hari ne a kauyukan Waga Mangoro da Garta, kana suka yi awon-gaba da matan.

Har yanzu dai ba a san adadin matan da aka sace ba.

Kauyukan na kusa da garuruwan Madagali da Michika , wadanda ke karkashin kungiyar ta Boko Haram.

Karin bayani