Kwalara ta kashe mutane 150 a Kamaru

Image caption Amai da gudawa ya yi yawa ne a Kamaru saboda rashin kula da muhalli

Rahotanni daga Kamaru sun nuna cewa sama da mutane 150 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar kwalara a arewacin kasar.

Wannan cutar ta fara kunno kai ne a lardin arewa mai nisam kana ta bazu har izuwa birnin Ngaoundere.

Hakan ne ya sa jami'an kiwon lafiya suka tashi tsaye wajen yin gargadi ga jama'a da su kiyaye irin ruwan da suke sha da kuma abincin da suke ci.

Bullar annobar kwalara ya zama wani al'amari na yau da kullum da yankin arewacin Kamaru yake fama da shi, sakamakon rashin kula da muhalli.

Karin bayani