Likita a birnin New York ya kamu da Ebola

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane sama da 4,800 sun mutu ya zuwa yanzu

An gano cewa wani likita wanda ya koma Amurka daga Guinea inda ya duba lafiyar masu fama da cutar Ebola ya kamu da cutar shi kansa.

Craig Spencer wanda ma'aikaci ne ga kungiyar Likitoci ta Medecins sans Frontieres, ya kamu da zazzabi ne bayan da ya koma gida daga Yammacin Afirka.

An dai garzaya da shi zuwa wani asibiti dake birnin New York a ranar Alhamis, kuma an killace shi.

Magajin garin New York ya ce babu wani abin damuwa, Yana mai jaddada cewa an bi dukkanin hanyoyin da suka dace akan mara lafiyar, kuma yace Likitan, ya gana ne da mutane uku kachal, kuma dukkaninsu a yanzu an sa musu ido.