An samu bullar cutar Ebola a Mali

Hakkin mallakar hoto

Gwamnatin Mali ta tabbatar da mutum na farko da ya kamu da cutar ebola.

Gwamnatin kasar ta yi shelar cewa wata yarinya me shekara biyu na dauke da kwayar cutar ebola.

Wannan shi ne karo na farko da za'a samu wani da ya kamu da cutar a Mali, dake makwabtaka da Guinea, daya daga cikin kasashen da cutar ta fi kamari.

Ana duba lafiyar yarinyar a garin Kayes dake yammacin Mali.

Rahotani sun ce a baya bayanan ne ta dawo daga Guniea.