Nigeria na bincike kan sace wasu mata

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana ci gaba da samun tashe- tashen hankula duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da sojoji suka ce an yi da 'yan Boko Haram

Gwamnatin Nigeria ta ce tana gudanar da bincike game da rahotannin da ke cewa mayakan Boko Haram sun sake sace wasu mata da kuma 'yan mata da dama a arewa maso gabashin kasar

Hakan na zuwa ne duk kuwa da sanarwar tsagaita wutar da sojojin kasar suka fitar.

Wani mai magana da yawun gwamnati a Nigeria, Mike Omeri, ya fadawa BBC cewa har yanzu jami'an tsaro na kokarin tantance ainihin abin da ya auku.

Wasu rahotannin dai na cewa an sace mata da 'yan mata 40.

An dai sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta tare da 'yan kungiyar ta Boko Haram a makon jiya amma tashin hankali na ci gaba da aukuwa a yankunan arewa maso gabashin kasar.

Har yanzu kuma babu alamun 'yan matan nan sama da 200 da aka sace watanni shidan da suka gabata, wadanda gwamnatin Nigeria ta ce za a saka.