Ebola: Za a samu magungunan gwaji

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An gudanar da gwaji a kan wasu mutane

Hukumar lafiya ta duniya-WHO ta ce za a iya samun kimanin magungunan gwaji na cutar Ebola dubu dari biyu zuwa tsakiyar shekara mai zuwa.

Wata jami'ar hukumar Marie-Paule Kieny, ta ce tuni aka fara gwada nau'o'i biyu daga cikin magungunan a jikin mutane a dakunan gwaji.

Tarayyar Turai ta sanar da bada karin kudade na yaki da cutar ta Ebola, inda yanzu zata bada gudunmuwar dala biliyan daya da miliyan dari biyu da hamsin.

Kimanin mutane dubu hudu ne dai cutar ta kashe zuwa yanzu.

Hukumomi a Mali suna sanya ido a kan mutane sama da 40 da suka yi mu'amulla da yarinyar da ta harbu da kwayar cutar Ebola, wadda ita ce ta farko da aka tabbatar ta kamu da cutar a kasar.

Goma daga cikin mutanen ma'aikatan lafiya ne.