'Boko Haram: 'Yan gudun hijira 800 sun rasu'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban yara da mata suna kwana a makarantu

'Yan gudun hijira kusan 800 sun rasu daga cikin dubbai da suka tsallaka garin Fotokol na Jamhuriyar Kamaru sakamakon rikicin Boko Haram a Nigeria.

Jami'in hudda da jama'a na karamar hukumar Ngala ta jihar Borno, Algoni Lawal wanda shima yake cikin 'yan gudun hijirar a can Kamaru, shi ne ya shaidawa BBC a cikin hirar da aka yi da shi.

Algoni Lawal ya ce "A takaice mutane kusan 800 sun mutu cikin watanni biyu tun da muka zo gudun hijira a Fotokol, a yau mun birne mutane 10. Mutane na kwana a waje babu abinci ga yunwa."

"Tallafin da gwamnatin jihar Borno ta aiko da shi ya kare a yanzu mutane na cikin wani irin yanayi", in ji Lawal.

A cewarsa, 'yan gudun hijirar suna fama da rashin cimaka da ta muhalli mai inganci abinda ke haifar musu da cutattaka, ga kuma rashin magani a cibiyar kiwon lafiya ta Fotokol.

Kawo yanzu hukumomi a Nigeria ba su maida martani ba game da wannan batun.