Faransa na tsaurara matakan soji a Mali

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai daruruwan dakarun Faransa a arewacin Mali

Faransa ta na kara tsaurara matakan soji a arewacin Mali domin hana abin da ta kira kara bullar ayyukan 'yan gwagwarmayar Islama.

Ministan tsaro na Faransa Jean-Yves Le Drian, wanda ke ziyara a Afrika ta Yamma, ya ce abu ne mai muhimmancin gaske ka da a bari mayakan gwagwarmayar Islamn su sake kama iko da yankin.

Ministan ya ce ofishin Majalisar dinkin duniya dake Mali shi ke da ikon kare yankunan kasar, to amma ita ma Faransa tana da rawar da za ta taka.

An kai sojojin Faransa malin ne a shekarar da ta wuce, bayan da mayakan Islaman suka kwace yankin arewacin kasar, amma tun lokacin Fransan ta rage sojojinta.