Jonathan zai sanar da takara a watan Nuwamba

Image caption Mr Jonathan na shan suka kan batun rashin tsaro

Shugaban Nigeria, Dr Goodluck Jonathan zai sanarda aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Shugaban kwamitin shirya sanarda takarar, Dr Bello Halliru ne ya bayyana haka a hirarsa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Sai dai ba tantance ba ko a wani dandali ne Mr Jonathan zai sanarda takarar ta shi ba.

Batun takarar Mr Jonathan na janyo cece-kuce a kasar inda tuni wasu suka garzaya kotu a kan cewar ba shi da hurumin sake tsayawa takara bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar.

Sai dai mukarraban Mr Jonathan sun ce kundin tsarin mulkin kasar bai hana shi tsayawa takara ba.

Gwamnatin Jonathan na shan kakkausar suka a Nigeria saboda tabarbarewar tsaro musamman a arewacin kasar da kuma zargin cin hanci da rashawa a cikin gwamnatin.