Zan tsaya takara a 2015 - Jonathan

Image caption Tuni aka lika fostocin Jonathan a biranen Nigeria

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan, ya bayyana sha'awarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben 2015.

Mr Jonathan ya shaida wa jiga-jigan jam'iyyar PDP cewa ya amince da tayin da 'ya'yan jam'iyyar suka yi masa na tsaya takarar shugabancin kasar a badi.

A kan haka ne shugaban ya nada kwamiti karkashin jagorancin tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Dr Bello Halliru domin tsara yadda zai bayyana aniyar takararsa a cikin watan Nuwamba.

Batun takarar Mr Jonathan na janyo cece-kuce a kasar inda tuni wasu suka garzaya kotu a kan cewar ba shi da hurumin sake tsayawa takara bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar.

Sai dai mukarraban Mr Jonathan sun ce kundin tsarin mulkin kasar bai hana shi tsayawa takara ba.

Gwamnatin Jonathan na shan kakkausar suka a Nigeria saboda tabarbarewar tsaro musamman a arewacin kasar da kuma zargin cin hanci da rashawa a cikin gwamnatin.