Za a hana 'yan gudun hijirar Syria shiga Lebanon

Hakkin mallakar hoto YASIN AKGUL DEPO PHOTOS
Image caption Miliyoyin 'yan gudun hijirar Syria na cikin kunci

Gwamnatin Lebanon ta ce za ta hana 'yan gudun hijira daga Syria tsallaka zuwa cikin kasarta, sai dai kawai a bisa dalilai na jinkai ko kuma wata matsala ta daban.

Daman tun bayan sama da wata daya hukumomin Lebanon din sun dauki matakan takaita shigar 'yan gudun hijirar sosai, abin da ya sa aka samu raguwar shigar sabbin 'yan gudun hijirar.

Ita dai Lebanon a yanzu tana da 'yan gudun hijrar na Syria kusan miliyan daya da rabi, wanda hakan ya zarta duk na wata kasa, da kuma yawan ya kai kusan sama da kashi daya bisa uku na gaba dayan al'ummar Lebanon din kanta.

Zuwan 'yan gudun hijirar ya takura tattalin arzikin kasar da kuma yanayin zamntakewar siyasa da tsaron kasar da daman ke dar-dar.