Sarauniya ta yi amfani da twitter a karon farko

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sarauniya ta yi amfani da fasaha wajen yin amfani da twitter a karon farko

Sarauniyar Ingila ta yi amfani da twitter a karon farko inda ta aike da sako ta hanyar @BritishMonarchy a lokacin da take kaddamar da baje kolin nuna kayan fasaha a gidan adana kayan tarihi na kimiyya dake London.

Baje kolin kayayyakin fasahar na daya daga cikin ayyukan da gidan adana kayayyakin tarihin ya yiwa shiri sosai.

Bayan kayayyakin tarihi da ake da su, masu ziyara za kuma su sami damar tattaunawa tare da ma'aikatan wajen.

Masu ziyara zasu ga irin ci gaban da aka samu ta fuskar fasaha.

Misali akwai kayan tarihi na aikewa da sakonni tun daga talgiram zuwa wayoyin tafi da gidanka.