Ebola: Mali ba zata rufe kan iyaka ba

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban kasar Mali Boubacar Keita ya ce ba za a rufe kan iyakar kasarsa da kasar Guinea ba bayan bullar cutar Ebola a Malin.

A ranar Juma'a ne wata yarinya 'yar shekaru biyu da ta shiga kasar Malin daga Guinea dauke da cutar ta mutu.

Amma kuma kasar Mauritania ta rufe kan iyakarta da Mali don neman hana yaduwar cutar.

Shugaban Malin ya ce zai yi duk abin da ya kamata wajen ganin cewa an kaucewa duk wata fargaba kan yaduwar cutar a kasar.

Ya kuma ce an dauki matakan kebe duk wadanda suka yi mu'amulla da yarinyar.

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya ta ce yawan mutanen da suka kamu da cutar Ebolan ya zarce dubu goma.

Ta ce alkalumma sun nuna cewa mutane 10,141 ne suka kamu da cutar, wadanda daga cikinsu ta halaka 4,922.

Hukumar ta ce akwai alamun cewa yawan wadanda cutar ta yi wa barna ya ma zarta hakan.

Rahoton hukumar ya ce kasar Laberiya ce cutar tafi yi wa barna, inda ta kashe mutane 2,705.

Sai kuma kasar Saliyo, inda mutane 1,281 suka mutu; kafin kasar Guinea, inda mutane 926 suka halaka.

Cutar ta kashe mutane takwas a Najeriya, sai daya a Mali da kuma daya a Amurka, inji rahoton.

Karin bayani