Fiye da mutane 10,000 ne suka kamu da Ebola

Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya ta ce yawan mutanen da suka kamu da cutar Ebola ya zarce dubu goma.

Ta ce alkalumma sun nuna cewa mutane 10,141 suka kamu da cutar, wadanda daga cikinsu ta halaka 4,922.

Hukumar ta ce akwai alamun cewa yawan wadanda cutar ta yi wa barna ya zarta hakan.

Bayanan sun zo ne a daidai lokacin da kasar Mali ke kokarin tinkarar cutar baya da ta kashe wata yarinya a kasar.

Shugaban Malin ya ce zai yi duk abin da ya kamata domin kawar da fargaba a kasar.

Yarinyar, 'yar shekaru biyu, wadda ta shiga kasar ta Mali daga kasar Guinea, ta mutu da cutar ne a ranar Juma'a.

Ana dai ta kokarin ganowa da kuma kebe duk wadanda suka yi mu'amala da yarinyar.

Rahoton hukumar lafiya ta duniyar ya ce kasar Laberiya ce cutar tafi yi wa barna, inda ta kashe mutane 2,705.

Sai kuma kasar Saliyo, inda mutane 1,281 suka mutu; kafin kasar Guinea, inda mutane 926 suka halaka.

Cutar ta kashe mutane takwas a Najeriya, daya a Mali da kuma daya a Amurka, inji rahoton.

Karin bayani