An rataye wata mace a Iran

Wani mutum da aak rataye a kasar Iran Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Iran ta yi kaurin suna wajen yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An rataye wata mace a Iran da aak sau da laifin kashe wani mutum da ake zargin ya yi yunkurin yi mata fyade.

Reyhane Jabbari mai shekaru 26 an rataye ta, duk kuwa da gangamin da aka yi a kasar da ma kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran Iran Tasnim ya rawaito cewa 'yan uwanta sun gagara daidaitawa da iyalan mamacin domin ceto Reyhane daga wanann hukunci.

Haka kuma ta kasa tabbatarwa da kotu cewar ta kashe mutumin ne domin kwatar kan ta daga aikata mata fyade.

An dai rataye ta da safiyar yau Asabar, kuma kafin hakan an bawa mahaifiyarta damar ganawa da ita na tsahon sa'a guda a jiya juma'a.

A yanzu shafin sada zumunta na facebook da aka bude musamman saboda gangami akan hukuncin da aka yanke mata, ba ka ganin komai baya ga ''Allah ya sa kin huta''.