'Yan adawar Nijar sun koka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan adawa a Nijar na caccakar gwamnati

'Yan adawa a Jamhuryar Nijar sun nuna rashin amincewarsu game da matakin da gwamnatin Kasar ta dauka na kara yawan 'yan majalisar dokoki

Kawancen jam'iyun siyasa na bangaren 'yan adawa na ARDR ya kuma zargi bangaren gwamnatin kasar da yunkurin shirya magudi a zabubuka masu zuwa ta hanyar kara yawan 'yan majalisar dokokin.

'Yan adawar sun yi zargin cewa gwamnati ta tura wannan bukata zuwa majalisar dokoki kai tsaye ba tare da daukacin 'yan siyasar kasar sun yi amanna da matakin ba kamar yadda aka saba.

Sai dai jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki a Nijar ta ce tsarin mulki ne ya bayarda damar kara yawan 'yan majalisa idan al'ummar kasa sun karu.

Sakataren yada labarai na jam'iyyar PNDS Tarayya ya shaidawa BBC cewa 'idan 'yan majalisa sun amince da wannan kari, za'a kara, idan basu amince ba, sai ayi watsi da wannan zance'.