An daure malami a Afghanistan a kan fyade

Image caption Kotu ta ki amince wa da hujjojin malamin

An yanke wa wani malamin addinin musulunci a Afghanistan hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari saboda samunsa da laifin yi wa wata yarinya mai shekaru 10 da haihuwa fyade.

Yarinyar ta je wani masallaci ne wurin malamin daukar karatu a lardin Kunduz lokacin da al'amarin ya faru.

Masu kare hakkin yarinyar sun ce fyaden da aka yi wa yarinyar ya yi muni domin an yi mata rauni da take bukatar tiyata.

Malamin, Mohammed Amin ya amsa laifin kwanciya da yarinyar, sai dai ya ce da amincewarta.

Kotun dai ta ki amince wa da hujjojin da malamin ya gabatar mata.

Mata masu fafutukar kare hakki, sun dauke yarinyar zuwa wani wuri don ka da iyayenta su halakata saboda zargin ta janyo musu abun kunya.