'Yan Boko Haram sun sace mutane 30

Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO BOKO HARAM
Image caption shekau ne jagoran Boko Haram

A wasu hare- hare na baya- bayan nan da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai a arewa maso gabashin Nigeria, an sace kananan yara kusan 30.

Shugaban al'ummar Mafa a jahar Borno ya ce an yi awon gaba da 'yan mata da shekarunsu suka haura 11, da kuma maza masu shekaru 13 zuwa sama daga kauyen .

A cewarsa, an kashe mutane 17 a lokacin da 'yan bindiga suka kai wa kauyen hari a ranar Alhamis.

Hakan na zuwa ne bayan da gwamnatin Nigeria ta ce ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Boko Haram.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch a wani rahoto ta ce daga shekara ta 2009 zuwa yanzu, 'yan Boko Haram sun sace mata da 'yan mata fiye da 500.