Dilma Rousseff ta lashe zaben Brazil

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dilma Rousseff ta yi kira da 'yan kasa su hada kai

An sake zabar shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff a wani wa'adin mulki na biyu, bayan zaben shugaban kasa mafi zafi da aka tabayi cikin shekaru da dama.

Ta lashe zaben da maki uku cikin dari a kan abokin hamayyarta, wanda tuni ya ce ya amince da sakamakon zaben.

A jawabin da ta yi wa cincirindon magoya bayanta, Ms Rousseff ta ce tana son yin fiye da abin da ta yi a baya, kuma ta ce babban abin da za ta mayar da hankali a kai yanzu shi ne sauye sauyen siyasa.

Shugabar ta yi kira ga 'yan kasar da su hada kansu, su kuma yi amfani da wannan karfi wajen kawo canji mai amfani.

Shugaba ta fuskanci zanga-zanga a bara, a kan cin hanci da rashawa da kuma kudaden da aka kashe a kan gasar cin kofin duniya.