An kafa sabuwar dokar soji a Masar

Image caption Shugaba Abdul Fattah al-Sisi na Masar

Shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya yi wata dokar soji da ta bai wa sojoji izinin kare muhimman gine-ginen gwamnati da hadin guiwar 'yan sanda.

An ruwaito kakakin shugaban Alaa Youssef, na cewa an yi sabuwar dokar ne da nufin kare muhimman kayayyaki da wurare da suka hada da cibiyoyin samar da wutar lantarki, da bututan iskar gas da rijiyoyin mai.

Masu lura da al'amura na ganin dokar za ta iya hada wa da jami'o'i, inda za a rika ganin sojoji na sintiri a kan tituna da kuma yuwuwar dawo da kotunan soji da ke yi wa farar hula shari'a.

Shugaban na Masar ya yi wannan doka ne bayan harin kunar bakin waken da aka kai yankin Sinai, inda aka hallaka sojoji sama da 30 a makon da ya wuce.