An kashe Bajamushe a Ogun

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban rundunar 'yan sandan Nigeria, Sulaiman Abba

'Yan bindiga a jihar Ogun da ke kudancin Nigeria sun kashe wani Bajamushe sannan kuma suka sace wani bature.

'Yan sanda a jihar ta Ogun sun tabbatar da lamarin wanda ya auku a garin Sagamu.

Kakakin 'yan sandan, Abimbola Oyeyemi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "Mutane hudu dauke da makamai ne suka kaddamar da harin."

Kamfanin Julius Berger ya ce mutumin da aka kashe dan kwangilarsa ne sannan kuma wanda aka sace din ma'aikacinta ne.

A cewar kamfanin an raunata ma'aikatansa biyu sakamakon lamarin.