Gwamnatin Nigeria ta gaza kan 'yan Chibok

Image caption 'Yan matan Chibok su na tsare a hannun Boko Haram fiye da watanni shida

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta zargi hukumomi a Nigeria da rashin gudanar da binciken da ya kamata a game da sace fiye da 'yan mata 200 na makarantar Chibok da kungiyar Boko Haram ta yi.

A cikin wani rahoto da ta fitar, kungiyar ta ce jami'an 'yan sanda a kasar sun nuna rashin damuwa sosai na tattara shaidu a game da sace 'yan matan, yayin da suke daukar lamarin wani karamin laifi.

Kungiyar ta ce 'yan Boko Haram suna tilastawa matan da suka yi garkuwa da su yin aure da sauya addini.

Rahoton Human Rights Watch ya ce ana kuma cin zarafin matan, da sa su aikin karfi, da yi musu fyade.

Kungiyar Human Rights Watch ta zargi jami'an tsaron Najeriya da take hakkin mutane da sunan yaki da 'yan kungiyar Boko Haram.

A baya dai, hukumomi a Nigeria sun sha musanta zargin jami'an tsaron kasar da take hakkin bil Adama.