Yaki da satar fasaha da yin kayan jabu a London

Hakkin mallakar hoto GETTY
Image caption Satar fasaha a London na janyowa gwamnatin Burtaniya asarar dimbin fama famai

Za a karawa baiwa jami'an 'yan sandan London dake kula sa laifukan da suka shafi kwaikwayon fasaha karin kudi

Wannan bangare na 'yan sandan kasar, shi ke gudanar da bincike na hakika akan matsalar satar fasaha da kuma yin kayayyakin jabu

Wannan sashe 'yan sanda zai sami karin £3m ta yadda zai iya gudanar da aiki har zuwa akalla shekarar 2016.

Ya karbi tsabar kudi sama da £2m, tun shekarar 2013 da aka kaddamar da sashen,

Wannan bangare na aikin 'yan sanda ya ce ya dakatar da wasu sunayen karya a internet har guda 2,359

Sannan ya kuma kwace kayayyakin jabu na kudaden da suka haura £1m tun watan Satumbar shekarar 2013

Hakkin mallakar hoto AFP

A ranar Alhamis da safe an tsare wani mutum mai shekaru 55 da wata mata mai shekaru 39 a Bury bisa zargin sayarda wasu kayayyakin kwamfita har 200,000 na jabu

Wannan bangare na 'yan sanda ya dukufa wajen takawa daidaikun mutane birki wadanda suke tunanin zasu iya kwaikwayon fasahar wani domin su sami kudi

Irin wadanna laifuka kuma na janyowa kasar asarar daruruwan miliyoyin fama famai in ji wani jami'in dan sanda a wannan sashe