APC za ta yi kwarya-kwaryar taro a Abuja

Shugabannin jam'iyyar adawa ta APC Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugabannin jam'iyyar adawa ta APC

A Nigeria, yau ne babbar jam'iyyar adawa ta APC za ta gudanar da wani kwarya-kwayar taronta na kasa a Abuja da nufin amincewa da wasu gyare gyare ga kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

Haka kuma ana sa ran taron zai amince da kundin manufofin jam'iyyar gabannin zabukkan shekarar 2015.

Jam'iyyar adawar tana kara samun kafuwa da karin magoya baya, na baya-bayan nan shine Shugaban Majalisar dokokin kasar Alhaji Aminu Waziri Tambuwal.

Karin bayani