Burtaniya za ta karfafa fannin hasashen yanayi

Britain Weather Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Na'urorin za su saukaka karantar yanayi

Kasar Burtaniya za ta kashe pam miliyan 97 domin sayen na'urorin da za su taimaka wajen karantar yanayi.

Ana sa ran na'urorin kwamfutocin da za a samar za su yi aiki ninki 13 fiye da wadanda ake amfani da su a yanzu.

A badi ne ake sa ran za a gina wurin da za ajiye kwamfutocin kana ya fara aiki zuwa watan Satumba mai zuwa.

Ofishin kula da yanayi na Burtaniya ya yi alkwarin samun ci gaba a fannin hasashen yanayi.

"Hakan zai bamu damar yin abubuwa a takaice kuma a bayyane da kuma samun bayanai karbabbu a fannin hasashen yanayi." In ji shugaban sashen hasashen yanayi, Rob Varley.

Ya kuma kara da cewa na'urorin za su iya bayar da damar a karanci yanayin wasu wurare da a da ake samun matsalar yin hakan.

"Hakan zai bamu damar zama shugabannin duniya ba ma kawai a fannin yin bayani akan yanayi ba, har ma a fannin yin hasashe." Varley ya kara da cewa.

Kamar yadda ofishin mai kula hasashen ya bayyana, kwamfutocin za su taimaka wajen samar da cikakkun bayanai game da gudun iska da yawan hazo da kuma saukar dusar kankara.